July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kungiyar IPMAN ta mayar da farashin man fetur 162

1 min read

Kungiyar masu gidajen mai masu zaman kansu ta kasa IPMAN, ta
umarci ‘ya’yanta su kara kudin farashin mai zuwa Naira 162 kan
kowace lita.
Ipman ta ce ta dauki wannan matakin ne sakamakon karin kudin mai da
gwamantin Najeriya ta yi zuwa N151.56k.
Wata sanarwa da reshen kungiyar na shiyyar kudu masu yamma ya fitar
ta ce ba su da wani zabi illa su kara kudin man domin gudun kada su yi
asara.
Shugaban kungiyar ta Ipman reshen Kano mai kula da wasu jihohin
arewacin Najeriya Alhaji Bashr Dan Malam ya ce dole ne su yi karin,
domin cike fansshe karin da za su samu daga wajen da suke sayo man
fetur din sakamakon matakin gwamnati na mayar da fetur din
N151.56k.
Wannan ne karo na uku da gwamnati take sauya farashin mai a ‘yan
watannin baya-bayan nan, sai dai sabanin wasu lokutan da ake rage
farashin, karin na man na wannan karon shi ne mafi yawa a baya-bayan
nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *