Kungiyar kwadago za ta tsunduma yajin aiki kan ƙarin kudin fetir da lantarki-hu Wabba
1 min read
Ƙungiyar ƙwadagon ta NLC ta yi kakkausar suka ga gwamnatin Najeriya
game ƙarin farashin mai da kudin lantarki, tana cewa wahalar da karin
zai haddasa za ta kare ne a kan talaka.
Ƙungiyar ta ce ta sha ba gwamnati shawarwari a kan yadda za a
inganta rayuwar jama’a amma ta yi biris da su, don haka za ta tattauna
da shugabannin rassanta don daukar matakin da ya dace.
Ku saurari hirar Ibrahim Isa da shugaban ƙungiyar ƙwadagon Kwamred
Ayuba Wabba.