June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sha’aban Ibrahim Sharada ya sha Mari a hannun wani matashi a wajen daurin aure a nan Kano

1 min read

Dan Majalisar tarayya mai wakiltar Birnin Kano Sha’aban Ibrahim ya sha marin ne, a yayin da ya halarci daurin Auren Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Kano,Alhaji Ali Haruna Makoda a Unguwar Gwammaja a Ranar Lahadin data gabata.
Lamarin ya faru ne, a dai-dai lokacin da Sha’aban Sharada ya ke gai sawa da mahalarta daurin auren a unguwar ta Gwammaja.
Buhari ya musanta zargin cewa daya daga cikin jami’an gwamnatinsa ya kamu da Corona
Wasu da al’amarin ya faru a kan idon su,sun shaidawa Jaridar Bustandaily cewa ba’a san musabbabin abinda ya hada matashin ba, da dan Majalisar.
To sai da wata majiya mai tushe ta bayyana cewa, matashin daya ne daga cikin magoya bayan Kwamishinan ayyuka na musamman na Jihar Kano,wato Muntari Ishaq,kuma tuni matashin ya cika wandansa da iska.

Buhari ya kirkiro da Ranar Matasa a Nigeria
Sai dai Jami’in tsaro sun kama wasu mutane goma wanda ake zargin yaran matashin ne.
Duk kokarin da Mukai naji daga bakin Sha’aban Ibrahim Sharada abin ya ci tura kasancewar bai ce komai a kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *