June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An gano maganin annobar Corona a Nigeria

1 min read

Masanin kimiyar halittun ya yi
ikirarin yana da maganin gargajiya na COVID-19 da ya
fi maganin kasar dake tashe na kasar Madagaska da
likitocin basu tabbatar da tasirin shi ba inganci –Sai dai
hukumomin lafiya sun yi gargadi da cewa, a yi taka
tsantsan, kuma tilas ne a gwada magungunan na
gargajiya kafin amfani da su in ba haka ba illarsu zata
yi muni fiye da amfanin su.
Masanin kimiyyar halittun Na Najeriya, Innocent
Ogbonna ya yi ikirarin cewa ya harhada maganin
gargajiyan da tsirrai.
Kamar yadda ya faru a Madagaska, tawagar da suka yi
bincike da Ogbonna sun yi ikirarin cewa, magani
gargajiyar su yana taimakawa marasa lafiyar COVID-19
su samu lafiya daga kwayar cutar.
Amma hukumomin kiwon lafiya sun yi gargadin cewa
ana bukatar gwaji kafin ayi amfani da magungunan
gargajiyar wajen jinyar COVID-19.
A cikin hirarshi da Muryar Amurka, Dr. Nathan Shehu,
likitane mai kula da cuttuka masu yaduwa a asibitin
koyarwa na jam’iyar Jos ya ce “Gaskiya akwai
magungunan gargajiya kuma za su iya yin maganin
COVID. Amma yana da muhimmaci kafin a fito da su
domin irin wannan dalili, dole ayi gwaje gwaje don
tabbatar da inganci ko suna aiki ko ba sa yi. Saboda kana
batun rayukan mutane ne.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *