July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnati ta saukakawa al’umma wajen tsadar kayan masarufi-Muhd Mahadi Inyas

1 min read

Limamin Masallacin juma’a na Sheikh Haruna Rashid dake Layin Baure a unguwar Rijiyar Lemo a nan Kano, Malam Muhammad Mahadi Inyas,ya ce rashin bada zakka da sakin dokokin addinin musulunci na daya daga cikin matsalolin rayuwa da al’umma suka tsinci kansu.

Malam Muhammad Mahadi Inyas ya bayyana haka ne a yayin Hudubar Sallar Juma’a daya gabatar a masallacin dake unguwar Rijiyar Lemo.

Malamin ya kuma bukaci Shugaban kasa Buhari da ya yi iya kokarinsa wajen kawo karshen tashin farashin kayan masarufi.

Haka zaka zalika ya kuma ce Allah ya yi alkawarin yiwa masu boye kaya domin Su tsauwalawa al’umma hukunci a gobe kiyama.

Malam Muhammad Mahadi Inyas ya ce da al’umma zasu ringa tallafawa marasa galihu dake unguwannin su da an sami saukin matsalolin rayuwa al’umma suka tsinci kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *