July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

NAJERIYA Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 22 da safiyar juma’a

2 min read

Mazauna garin da Muryar Amurka ta yi hira da su sun
bayyana cewa, i zuwa lokacin hirar, hukumomi basu riga sun
isa inda lamarin ya faru ba, suka kuma ce gawarwakin ‘yan
bangar suna daji ba ayi jana’izarsu ba.
A can garin Dukku dake yankin
Karamar Hukumar Rijau kuwa, Maharan sun hallaka
‘yan banga 17 bayan wani dauki ba dadi da suka yi da
su a lokacin da maharan suka yi yunkurin shiga garin
na Dukku.
Mazauna garin da Muryar Amurka ta yi hira da su sun
bayyana cewa, i zuwa lokacin hirar, hukumomi basu
riga sun isa inda lamarin ya faru ba, suka kuma ce
gawarwakin ‘yan bangar suna daji ba ayi jana’izarsu
ba.
Duk Kokarin jin ta bakin Rundunar yan sandan jihar
Nejan akan kannan al’amari da wakilinmu yayi, yaci
tura domin kuwa kakakin yan sandan jihar, ASP Wasiu
Abiodun bai dauki waya ba kuma bai maida martani
sakon wayar hanu da aka aika mashi ba .
Sai dai gwamnatin jihar Nejan ta tabbatar da aukuwar
wannan al’amari. Kwamishinan Labarai na jihar Nejan
Alh.Sani Abubakar bayan jajantawa wadanda lamarin
ya shafa yace, gwamnati na iya kokarinta wajan kawo
karshen wannan tashin hankali.
Ya kara da cewa, “ saboda wadannan abubuwa da suka
faru, yasa kowa cikin halin jimami. Akwai matakai da
muka dauka na nan da nan da ba zamu bayyana ba
saboda dalilan tsaro, yawanci idan aka bar shi a sirrance
ya fi tasiri. Amma ina so in tabbatar wa al’umma cewa
gwamnati ta dau matakai dai dai gwargwado.”
A halinda ake ciki dai, yanzu haka akwai gwamman
mutane a garin na Kagara da wadan nan ‘yan bindiga
suka yi awon gaba da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *