June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ruwan sama ya rusa sama da gidaje dubu 50 a Jigawa

3 min read

Hukumomi a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya sun tabbatar da
mutuwar mutum goma sha tara sannan fiye da gidaje dubu hamsin
sun rushe sakamakon mamakon ruwan sama da ya haddasa
ambaliyar ruwa a sassan jihar.
Lamarin dai ya haddasa salwantar dukiyoyi a kananan hukumomi
goma sha bakwai daga cikin ashirin da bakwai na jihar.
Al’amarin dai na zuwa ne bayan shafe makwanni ana tafka ruwan
sama kamar da bakin kwarya.
Al’umomin garuruwan Babaldu da Shingurin da Samamiya da ke
yankin karamar hukumar Birnin Kudu a jihar ta Jigawa, na cikin tsaka
mai wuya sai dai lamarin ya fi muni a garin Shingurin wanda yanzu
haka wani kogi da ya tumbatsa ya tasamma tashin garin
ɗungurungum.
Baya ga rusa gidaje da lalata amfanin gona, har rasa rai wannan
iftila’i ya haddasa inda wani matashi ya rasa ransa a garin na
Shingurin.
Ruwan sama ya haddasa ambaliyar ruwan data lalata amfanin gona a
Jigawa
Alhaji Umar Aliyu shi ne mahaifin matashin ya kuma shaida wa BBC
cewa, yaaon nasa ya je kai taimako ne gidan kanin mahaifin nasa a
nan ne kuma sai gini ya rufta masa anan ne kuma sai ya nitse a
ruwan da ya zama kamar kogi.
Mahaifin matashin ya ce “Tun da ruwa ya tafi da shi ba a ganshi ba
sai bayan kwana hudu, sannan aka gano gawarsa a wani gari can
daban”.
A yanzu haka dai daruruwan iyalai ne wadanda suka tsira daga
gidajen su suka sami mafaka a gidajen ‘yan uwa da makarantu da
masallatai, yayin da wasunsu kuma suka ci gaba da zama a gidajen
nasu duk da mamayewar da ruwan ya yiwa ciki da wajen gidajen
nasu.
Malam Abubakar Garba Haske na daga cikin mutanen da suka rasa
gidajensu ya kuma shaida wa BBC cewa, “Yanzu a makaranta nake
kwana, muna da gidajenmu da wasu kayan abincinmu duk sun
lalace, kai hatta tufafinmu duk sun lalace saboda tsabar ruwan sama
wanda ya yi sanadin rushewar gidajenmu”.
Kwana a makarantu da masallatai
Wakilin dagacin Shingurin Malam Alhassan Abdu, ya ce bai taba
ganin iftila’i irin na wannan shekarar ba, komai da suka shuka na
amfanin gona ruwan ya lalata.
Alhaji Yusuf Sani Babura, shi ne shugaban hukumar bayar da agajin
gaggawa a jihar Jigawa, ya kuma shaida wa BBC cewa, babban abin
da ya fi tayar musu da hankali yanzu shi ne irin yadda gidaje ke
rushewa akasari a kauyuka.
Ya ce “A yanzu muna adadin gidajen da muka tabbatar sun rushe
saboda ruwan sama a sassan jiharmu sun kai sama da dubu hamsin
da daya, sannan kuma muna da labarin cewa akwai wadanda ke
kwana a makarantu da masallatai saboda rashin matsunni”.
Alhaji Yusuf Sani Babura, ya ce ba su da labarin abin da ya faru a
Shingurin don ba a kawo musu rahoto ba, to amma tun da yanzu sun
samu rahoton iftila’in da suka shiga, za a kai musu dauki na
gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *