June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje ‘5,200’ a wasu ƙauyukan Kano

1 min read

Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar mutuwar mutum huɗu da kuma raba mutum 5,200 da muhallansu a jihar Kano, kamar yadda Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito. Lamarin ya faru ne a ƙananan hukumomin Rogo da Danbatta, biyo bayan ruwan saman da aka yi mai ƙarfi. A Rogo, mutum biyu sun mutu inda kuma ruwan ya lalata kusan gidaje 200, a Danbatta kuma, mutum biyu aka tabbatar da mutuwarsu inda kuma ruwan ya lalata sama da gidaje 5,000, kamar yadda jairdar ta ruwaito. Ko a makon nan sai da wasu mata da ƙananan yara takwas suka mutu sakamakon kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke ƙaramar hukumar Jega ta Jihar Kebbi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *