July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An zargi sojojin ƙasar da kashe fararen hula 70

2 min read

Hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta Jamhuriyyar Nijar ta zargi
sojojin ƙasar da kashe gwamman fararen hula a yayin wasu hare-
hare na ƙoƙarin daƙile harin ta’addanci.
Ta ce ta gano fiye da gawarwaki 70 a wasu manyan ƙaburbura shida
a Tillaberi da ke arewa maso yammacin ƙasar, wani yanki da hare-
haren masu tsattsauran ra’ayi ya shafa.
Ana zargin an yi kashe-kashen ne a farkon wannan shekarar. Ɗaya daga cikin masu binciken ya ce an kashe fararen hular ne da
makamai irin su takobi da adduna da kuma wasu ƙananan makaman.
Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan Adam na duniya sun zargi sojojin Nijar
da Mali da kuma Burkina Faso da kashe gwamman mutane ba bisa
ƙa’ida ba a yayin da suka kai wa masu ayyukan ta’addanci hare-hare
a yankin Sahel.
Hukumar kare hakkin ɗan Adam ta Nijar tana bincike kan zarge-
zargen cewa fararen hula 102 sun ɓata a yankin da ke fama da rikici
tsakanin 27 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afrilu bayan wani harin
sojoji.
“Tabbas an kashe fararen hula kuma an gano gawarwakin aƙalla 71 a
wasu manyan ƙaburbura,” a cewar Abdoulaye Seydou, shugaban
wata cibiya ta kawo zaman lafiya da cigaban dimokraɗiyya a Afrika,
wadda da hannunta cikin binciken.
Ya ƙara da cewa: “Akwai hannun Rundunar Dakarun Tsaro ta (FDS)
kan waɗannan kashe-kashe.”
Amma Mr. Seydou ya ce ba zai yiwu a faɗi ko da hannun manyan
sojoji a ciki ba.
Har yanzu babu wani martani daga hukumomin Jamhuriyyar Nijar
kan zargin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *