Kungiyar Bakin Bulo ta bukaci Shugaban Kasa Buhari ya sauka daga mukaminsa
1 min read
Kungiyar bakin Bulo Network For Better Tomorrow ta bukaci Shugaban Kasa Buhari daya sauka daga mukaminsa shugaban kunhiyar Kwamarad Bilal Nasidi Mu’azu ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a daren jiya.
Kwamarad Bilal Nasidi Mu’azu ya ce ganin irin yadda a kasar ke fama da matsalar tsaro da sace-sacen Mutane da fyade ka mata yayi Shugaban ya sauka a sakamakon gazawarsa.
Haka zalika kungiyar ta kuma bukaci Shugaban kasa da ya cire karin kudin wuta dana manfetir da gwamnatin ta kara data gaggauta cirewa.
Da yake jawabin Babban sakatare a kungiyar kwamarad Muhammad Sa’id Abdullah ya bukaci kungiyoyi da sauran al’umma dasu san irin mutanan da ya kamata su zaba a zaben shekara ta 2023 domin fitar da kasar nan daga halin data tsinci kanta a aciki.
A baya-bayannan ne gwamnatin Nigeria ta sanar da karin kudin manfetir dana wutar lantarki hadi da tashin farashin kayan masarufi a kasar.
Jaridar bustandaily ruwaito kungiyar na duba yihuwar gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin a mincewarsu da karin farashin.