July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yaki Sun Yi Luguden Wuta a Dazukan Kaduna

2 min read

Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce
Rundunar Kai Farmaki ta Thunder Strike ta yi ta barin
wuta akan wasu sansanonin yan bindiga biyu a jihar
kaduna.
Hare Haren da jiragen yakin kasar suka kaddamar a
dazukan Kuduru da Kwiambana a jihar ta Kaduna sun
yi sanadin kashe ‘yan ta’adda da dama a dazukan.
Kwamandan Dakarun Ruwa (Navy Commander)
Abdulsalam Sani na Hedikwatar tsaron kasar ya shaida
wa muryar Amurka cewa jiragen yakin, kazalika sun
rugurguza sansanonin ‘yan ta’addan.
Hedikwatar tsaron Najeriyar ta ce hare haren za a ci
gaba da kai wa ne har sai an kawo karshen aika aikar
‘yan bindigar a sassan jihar.

Jiragen Yakin sojojin saman Najeriya samfurin Alpha Jet
ke Atisayen kayatar da manyan baki Inda suke fitar da
Hayaki kore da fari da kore wato launin tutor Najeriya
Kwamanda sani ya kara da cewa wannan na zuwa ne
bayanda a makon jiya su ma sojojin kasa sukai wa
wasu masu garkuwa da mutane kwanton bauna, inda
suka halaka hudu daga cikinsu.
A bangarenta, gwambatin jihar kaduna, ta bakin
kwamishinan harkokin tsaro na jihar, Samuel Aruwan
ta yaba da wannan ci gaba, inda shima ya tabbatar da
za a ci gaba da kai hare haren.
Aruwan ya ja hankalin jama’ar jihar cewa kalubalen
tsaro da jihar ke fuskanta bai da alaka da addini ko
kabilanci, inda yace aika aika ne kurum na ‘yan
ta’adda, kuma gwamnati na aiki tukuru don yi wa
tubkar hanci.
Inda ya bayyana kwarin gwiwar maido da cikakken
zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar nan bada
jimawa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *