March 5, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutanen da aka yanke wa hukuncin kisa a jihar a 2020

2 min read

Bayanan da BBC Hausa ta samu sun nuna cewa mutum tara aka
yanke wa hukuncin kisa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya daga
watan Janairu zuwa watan Agustan 2020.
Takardun kotuna daban-daban da BBC Hausa ta samu sun nuna
cewa an yanke hukunce-hukunce kan mutanen ne bayan samunsu
da hannu a aikata mabambanta laifuka.
A shirye nake na sa hannu kan hukncin kisa ga wanda ya yi batanci ga Annabi
An samu bakwai daga cikinsu da aikata kisan kai, mutum ɗaya ya
aikata fyaɗe yayin da aka kama ɗaya da laifin ɓatanci ga Annabi
Muhammadu (SAW).
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta ce Matashin da Mahaifinsa ya rufeshi shekara 15 yayi ne da niyyar Kisan kai
A makon jiya ne gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sha
alwashin sanya hannu kan takardar kashe Yahaya Sharif-Aminu, An yanke hukuncin farko ne ranar 11 ga watan Fabrairu, inda za a
kashe Ali Abdullahi ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kisan
kai. Ga jerin mutanen da aka yanke wa hukuncin kisan:
Ali Abdullahi
Kotu mai lamba Shida ta kama shi da laifin kisan kai inda ranar 11 ga
watan Fabrairu aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Yakubu Ɗalha
Shi ma Yakubu Kotu mai lamba Shida ce da ke birnin Kano ta kama
shi da laifin kisan kai, kuma ranar 3 ga watan Maris ta yanke masa
hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Abdullahi Isyaku
Babbar Kotun Kano ta same shi da laifin kisan kai kuma ta yanke
masa hukuncin kisa ta hanyar rataya ranar 16 ga watan Maris.
Mujahid Sa’id
Kotu mai lamba 13 ta same shi da laifin kisan kai inda a ranar 24 ga
watan Maris ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Naziru Ya’u
Kotu mai lamba Ɗaya ta same shi da laifin aikata kisan kai inda ta
yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya ranar 13 ga watan Yuli.
Shehu Ado Shehu
Kotu mai lamba Shida ce a Kano ta same shi da laifin kisan kai kuma
a ranar 26 ga watan Yuni ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar
rataya.
Isah Auta
Kotu ta mai lamba Ɗaya ta yanke hukuncin kisa ta hanyar ratayewa a
kan Isah Auta bayan ta kama shi da laifin kisan kai. An yanke masa
hukuncin ne ranar 29 ga watan Yuni.
Yahaya Aminu
Babbar Kotun Shari’a ta jihar Kano ce ta same shi da laifin yin
ɓatanci da Annabi Muhammadu (SAW), inda ranar 10 ga watan
Agusta ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Mati Abdu
Shi ma Babbar Kotun Shari’a ta Kano ta kama shi da laifin fyaɗe
kuma ranar 12 ga watan Agusta ta yanke masa hukuncin kisa ta
hanyar jefewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *