July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Siyasa da addini ne ‘suka hana shawo kan rikici a Kudancin Kaduna’

2 min read

A jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya masu ruwa da tsaki na ci
gaba da nuna damuwa kan rikice-rikice masu nasaba da kabilanci
da addini da suka addabi yankin kudancin jihar.
Tsohon mataimakin gwamnan jahar Barnabas Bala Bantex ya shaida
wa BBC cewa ana amfani da siyasa wurin raba kan al’umma, wanda
ke ci gaba da rura wutar rikicin addini da na ƙabilanci.

An kashe mutane 33 a Zangon-Kataf a Kaduna
Ya ce ba shakka akwai mutanen da ke amfani da rikicin don samun
riba a siyasar su.
Tsohon mataimakin gwamnan ya ce yana takaicin baza sojoji a
kudancin jahar, wanda a cewar sa hakan zai hana ‘yan kasuwa
shigowa jahar don zuba jari.
Kungiyoyin Addinai Sun Nemi Hanyar Shawo Kan Rikici a Jihar Kaduna

A kan haka yake ganin dole ne masu ruwa da tsaki a cikin al’umma
su hadu wuri ɗaya don samar da mafita.
Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya mafi fama da matsalolin
tsaro kama daga hare-haren ‘yan fashin daji a yankin Birnin Gwari da
kuma rikicin ƙabilanci musamman a yankin Kudanci.

Sojojin Najeriya sun tarwatsa ‘yan fashi a Kaduna.
Kimanin shekara 40 ke nan ake ta fama da wannan rikici na
Kudancin Kaduna, kuma lamarin na so ya gagara.
Ko a baya-bayan nan, rahotanni sun ce an kashe gomman mutane a
rikicin ta hanyar kai hare-hare masu kama da na sari-ka-noƙe a
yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *