June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ambaliya ta raba mutane miliyan 2 da gidajensu

1 min read

Jami’an gwamnati a arewacin Najeriya sun ce mutane miliyan biyu
ne ambaliyar ruwa ta raba da gidajensu bayan an bude wadansu
madatsun ruwa biyu da suka cika suka batse kuma ake fargabar za
su ci yankunan da ke kusa da su.
Ruwan da ya fito daga madatsun ruwan Callawa da Tiga a Jihar Kano
dai ya malala zuwa yankunan da ke kwari a Jihar Jigawa.
Yanzu haka dai ana ci gaba da tsugunar da mazauna kauyukan da
ambaliyar ruwan ta shafa.
Jihohi da dama na Najeriya ne dai suka fuskanci ambaliyar ruwa
sakamakon dimbin ruwan saman da aka samu cikin watanni biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *