June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kayyade farashin buhun shinkafa a Kano

1 min read

Gwamnatin Kano ta hannun hukumarta ta sauraron
korafe-korafen jama’a da kuma yakar cin hanci da
rashawa ta cimma yarjejeniya da kungiyar masu sarrafa
shinkafa ta kasa dake jihar, kan kayyada farashin buhun
shinkafar mai nuyin kilogiram 50 kan naira dubu 16.
Rahotanni sunce an rattaba hannu kan yarjejeniyar kayyade farashin
buhun shinkafar a hedikwatar hukumar sauraron korafe-korafen
al’ummar ta Kano, bayan ganawa tsakanin shugabanta Barista
Muhuyi Magaji Rimingado da shugaban kungiyar masu sarrafa
shinkafa na Najeriya, reshen Kano Alhaji Muhammad Abubakar
Maifata.
A karkashin yarjejeniyar, kungiyar masu sarrafa shinkafar za su rika
shigar da tirela 30 makare da shinkafa a kowane mako, inda za a
rika saidawa shagunan saida kayayyaki a sassan jihar kan farashin
naira dubu 15, 500 bisa kowane buhu guda, yayinda su kuma
shagunan za su rika saidawa jama’a buhun shinkafar kan farashin
naira dubu 16,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *