June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Miyetti Allah ‘za ta zauna lafiya da maƙwabtanta’ a Kudancin Kaduna

1 min read

Ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah reshen Jihar Kaduna ta ce ta yanke
shawarar rungumar zaman lafiya da sauran ƙabilu a Kudancin Kaduna.
Ƙungiyar mai cikakken suna Miyetti Allah Cattle Breeders Association
of Nigeria (MACBAN), ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwar bayan
taro da ta fitar a Kafanchan ranar Lahadi.
Shugaban ƙungiyar na jiha Malam Hassan Tugga da kuma na yankin
Kudancin Kaduna Malam Abdulhamid Musa da sauran manyan jami’ai
ne suka sanya wa sanarwar hannu.
“Mun yanke shawarar komawa kan turbarmu ta asali ta zaman lafiya da
maƙwabtammu na Kudancin Kaduna,” a cewar sanarwar, kamar yadda
kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito.
“Mun yarda mu zama ‘yan uwan juna domin samar da cigabaa yankin.
Muna kira ga mutanemmu da su daina ƙyale yara ƙanana suna yin kiwo
domin gudun haifar da tashin hankali da kuma lalata amfanin gona.
“Kazalika, muna kira ga manoma da su daina toshe burtali (hanyoyin
kiwo) a ko’ina.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *