July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wata a Jihar Kano Kotu ta zartar da hukuncin Kisa akan wani tsaho da ya yiwa yarinya fyade

2 min read

Wata kotun addinin Musulunci da ke jihar Kano a arewacin Najeriya
ta yanke hukuncin kisa kan wani tsoho da aka samu da laifin yi wa
wata yarinya fyade.
Alkalin kotun, Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, ya ce za a kashe
mutumin, mai suna Mati Audu mai shekara 70, ta hanyar rajamu.
Kotun ta samu mutumin, wanda dan karamar hukumar Tsanyawa ne,
da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyade.
Mati Audu ya tabbatar wa kotun cewa shi ne ya aikata laifin, kuma
sau hudu ana dage shari’ar domin alkali ya ba shi dama ko zai sauya
matsayinsa, sai dai duk lokacin da aka koma kotu yana jaddada mata
cewa shi ne ya yi wa yarinyar fyade. Amma ya bukaci a yafe masa.
Daga nan ne alkali Ibrahim Sarki Yola ya karanto sassan Al-Kur’ani
mai tsarki da kuma wasu hadisai wadanda suka nuna girman laifin
da ya aikata, sannan ya yanke hukuncin kisa ta hanyar rajamu bisa
ambato sashe na 127(b) na kundin shari’ar Musuluncin jihar ta
Kano.
Matsalar fyade na neman zama ruwan dare a jihar ta Kano da ma
wasu sassan Najeriya lamarin da ya sa wasu ke ganin ya kamata a
rika daukar tsauraran matakai a kan masu aikata wannan babban
laifi.
Ko a watan jiya sai da ‘yan sandan jihar suka gurfanar da wani
mutum da ake zargi da yi wa mata 40, ciki har da mai shekara 80
fyaɗe a Kano a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *