September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Samarin Jihar Kano sun fison auren ‘ya’yan masu kudi a cewar wani rahoto

1 min read

Masu dalilin aure sun gano cewa matasa na nuna sha’awar auren
matan da ke da gidan kansu, yayin da su kuma matan suka fi
sha’awar auren masu aikin kaki kamar sojoji da kwastam.

A cewar rahoton samarin na kano na da burin auren macen da take da abin hannu ko iyayenta suke da abin hannu.

Rahoton ya kuma ce samarin na kano na da burin auren mace mai Fara doguwa mai gashi,kamar yadda wasu matasa suka shaidawa jaridar bustandaily.

A jihar kano dai ana yawan samun sake-saken aure,inda hakan ya haifar da samun zaurawa barkatai.
Bugu da kari kuma akwai tarihin ‘yan mata marasa aure.

Hajiya hafsa Ahmad mai dalilin aure
da ke zaune a bacirawa a jihar Kano, wadda ta shafe sama da shekaru arba’in tana hada aure ta ce lamarin akwai abin mamaki musamman yadda samarin ke da buri kala-kala

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *