July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Saudiyya ta soke hukuncin kisan waɗanda suka kashe ɗan jaridar Jamal Khashoggi

2 min read

Wata kotu a Saudiyya ta rage hukuncin kisan da aka yanke wa
mutum biyar da aka samu da laifin kisan gillar da aka yi wa Jamal
Khashoggi a 2018.
Masu shigar da ƙara sun ce an mayar da hukuncin zuwa zama
kurkuku na shekara 20 bayan da iyalan mamacin suka yafe wa
mutanen da suka hallaka ai gidan nasu.
Amma matar da yake shirin aura kafin aka kashe shi ta ce shari’ar
“wasan yara ce.”
An dai kashe Khashoggi ne a cikin ƙaramin ofishin jakadancin
Saudiyya da ke Santanbul , kuma mutanen da suka kashe shi jami’an
gwamnatin Saudiyyar ne.
An kuma san shi da sukar lamirin gwamnatin ta Saudiyya.
Hukumomin ƙasar sun ce an kashe shi ne ba tare da saninsu ba,
kuma bayan shekara guda ƙasar ta gurfanar da mutum 11 a gaban
wata kotu tana tuhumarsu da aikata kisan. Wata hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman ta yi watsi da
shari’ar gabi ɗayanta. Shugabar hukumar Agnes Callamard ta
bayyana cewa “Da gangar aka kashe Khashoggi kuma kisan na gilla
ne.”
Ms Callamard ta kuma ce akwai kwararan shaidu da suka tabbatar
manyan jami’an gwamnati har da Yarima Mohammed bin Salman na
da hannu dumu-dumu cikin kisan.
Yariman ya musanta aikata laifin amma wasu masu yi ma sa hidima
su biyu na fuskantar shari’a a Turkiyya a bayan idonsu, akwai kuma
wasu mutum 18 da Turkiyya ke tuhuma da aikata mummunan laifin.
Dan marigayi Khashoggi Salah ya gana da Sarkin Saudiyya da Yarima
Mohammed makonni bayan kisan mahaifin nasa
Kafofin yada labarai mallakin gwamnatin Saudiyya sun bayyana
wannan hukuncin a matsayin na karshe da ka yanke wa mutanen da
aka samu da laifin kisan Jamal Khashoggi – tsohon dan jarida dan
kasar ta Saudiyya da ya rika sukar lamirin yarima mai jiran gadon
sarauta Mohamed bin Salman.
A farkon wannan shekarar iyalan gidan marigayi Khashoggi suka
bayyana cewa sun yafe wa wadanda suka kashe mai gidan nasu,
kuma sun ce sun yi amanna cewa ba da gangar aka kashe shi ba.
Wannan ne matakin da ya share fagen rage tsaurin hukuncin kisan
da aka yanke wa mutanen da aka samu da aikata wannan
mummunan laifin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *