March 24, 2023

Gwamnatin Najeriya ta amince da buƙatun masu zanga-zanga

1 min read
Share

Kwamitin gyara ayyukan ‘yan sanda a Najeriya da sugaban ƙasa ya kafa ya amince da buƙatu biyar na masu zanga-zanga a ƙasar da aka kwashe kwanaki ana yi.
Daga cikin buƙatun da suka nema akwai sakin dukkanin ‘yan zanga-zangar da aka kama da kafa kwamitin gyara ayyukan ‘yan sanda da ƙara wa ‘yan sandan albashi tare da yi musu gwajin lafiyar ƙwaƙwalwa.
Sanawar da mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa Femi Adesina ya fitar a yau Talata ta ce Sufeto Janar Mohammed Adamu ya gana da mahukunta, inda suka amince da buƙatun.
Ganawar tasu ta biyo bayan umarnin da Shugaba Buhari ya bayar na rushe rundunar SARS mai yaƙi da fashi da manyan laifuka bayan ‘yan Najeriya sun buƙaci hakan bisa zargin cin zarafi da kisan mutane ba bisa doka ba.
An gudanar da ganawar ce ƙarƙashin jagorancin Sufeto Mohammed Adamu da kuma Hukumar Kare Haƙƙi ta Ƙasa, inda shugabannin ƙungiyoyin farar hula da mawaƙa da taurarin fina-finai suka halarta gami da wakilan masu zanga-zangar #EndSars.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Copyright © All rights reserved. | Newsphere by AF themes.