March 24, 2023

Ɓarayi 5 sun haɗu da ajalinsu a hannun wasu matasa a Kaduna

1 min read
Share

Wasu fusatattun matasa a Kaduna sun kashe ɓarayi biyar a
Ƙananan Hukumomin Sanga da Lere, kamar yadda
kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel
Aruwan ya tabbatar.
Tun da farko dai, biyu daga cikin ɓarayin sun kai wa wani ɗan
kasuwa hari inda suka ƙwace masa kuɗaɗe a Fadan Karshi da
ke Sanga.
Sai dai ko da jami’an tsaro suka isa inda lamarin ya faru sai
suka tarar da wasu fusatattun matasa sun ƙona ɓarayin
ƙurmus.
Kwamishinan ya ƙara da cewa a Ƙaramar Hukumar ta Sanga
dai, wasu ‘yan bindiga sun ɓude wa motoci wuta kan hanyar
Aboro zuwa Kafanchan.
A yayin da suke harbin, sai harsashi ya sami wani mai suna
Richard Sabo wanda ya kaɗe ɗaya daga cikin ɓarayin da mota
bayan motar ta ƙwace masa.
A Ƙaramar Hukumar Lere kuma wasu matasa ne da suka
shahara wurin satar dabbobi su ma suka haɗu da ajalinsu a
wurin fusatattun matasa.
Kwamishinan ya bayyana cewa an bi ɓarayin su uku inda aka
ci ƙarfinsu a ƙauyen Domawa, inda a nan ne matasan suka
kashe su.
A cewar kwamishinan, Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya ja
hankalin matasan jihar da su guji ɗaukar doka a hannunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Copyright © All rights reserved. | Newsphere by AF themes.