April 25, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

MATSALAR TSARO A Najeriya: An Maka Buhari A Kotu

2 min read

Tsohon dan takardar gwamna a Jamiyyar
AAC ( African Action Congress) a Jihar
Adamawa da Ke Arewa Maso Gabashin
Najeriya, Alhaji Auwal Uba ya maka shugaba
Mohammadu Buhari a kotu saboda cigaba da
rike shugabanin tsaron kasar duk da cewa
sun gaza shawo kan matsalar tsaro da ke
addabar Kasar.
A wata hira ta musamman
da yayi da muryar Amurka a Abuja, tsohon dan
takaran ya ce ba shugabanin tsaron kadai ya Ke
so a cire ba.
Alhaji Auwal A. Uba ya shigar da karar a gaban
babbar Kotun Taraiyya da ke Abuja inda ya roki
kotun da ta umarci shugaba Buhari da ya sauka
daga kan kujerar mulki da shi da dukan
shugabanin hukumomin tsaron kasar baki daya.
dole-ne-yan-sanda-su-sake-salo-wajen-yaki-da-
yan-bindiga-igp
zamu-ga-bayan-masu-garkuwa-da-mutane-don-
neman-kudin-fansa—burutai
wasu-yan-najeriya-na-alakanta-matsalar-tsaro-
da-sakacin-gwamnati
A.A.Uba ya ce ya dauki matakin ne a madadin
shiyar Arewa wadanda ke fama da rashin tsaro
tun tsawon shekarun da Shugaban Buhari ya ke
mulki.
Uba ya ce baya ga wadannan bukatun kuma,
yana son gwamnatin tarayya ta biya Naira
Biliyan 100 ga wadanda abin ya shafa a
matsayin diyya.
Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Tsaro a Sokoto
Daya cikin Shugabanin kungiyar Muryar talaka
Saleh Bakoro sabon feggi ya ce Shi bai amince
da Kiran shugaba Buhari ya sauka ba, amma
yana so a chanja Shugabanin Hukumomin tsaro
saboda sun dade akan mukaman nasu har sun
zama babu sauran dabarun kawar da ‘yan
ta’adda da masu tada kayar baya.
Shi Kuwa kwararre a fanin Shari’a Barista
Abdulqadir Alhaji Sani ya ce shigar da kara
akan wani abu da dan kasa yake ganin bai
gamsu da shi ba, dama ce da dokar kasa ta
bayar, saboda haka wannan yunkuri da aka yi
na shigar da kara saboda tsaro, ya yi daidai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *