March 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin tarayya ta umarci gwamnatin Kano ta sake bude cibiyoyin gwajin Korona

1 min read

Gwamnatin tarayya ta umarci jihar Kano da sauran jihohin kasar nan da su sake bude dukkanin dakunan gwaje-gwajen Covid-19 da aka rufe a baya.

Bustandaily ta ruwaito shugaban kwamitin kartakwana na fadar shugaba kasa kan annobar Covid-19 Boss Mustapha ne ya bada umarnin biyo bayan bullar annobar a karo na biyu ranar Talata

Boss Mustapha ya.

Ya ce rahotanni da ke iskesu ya nuna cewa mafiya yawa daga cikin cibiyoyin gwaje-gwajen basa yin aiki yadda ya kamata.

Ya kuma ce daga ranar daya ga watan janairun shekara mai kamawa za a fara bayyana sunayen matafiyan da suka ki yadda a yi musu gwajin na Covid-19.

Masarautar Rano ta dakadar da dagatai biyu da suka sace tallafin Korona

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 14 ga Disambar da muke ce ne cutar covid-19 ta sake bullowa a karo na biyu.

Hakan kuma ta sanya tuni hukumomi suka fara daukan mataki domin ganin bata yadu kamar yadda ya yi a farkon zuwanta ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *