March 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Katin ɗan ƙasa: Abin da ya sa Pantami ya dakatar da wasu ma’aikatan NIMC

2 min read

Ministan sadarwa na Najeriya Dakta Isa Ali Pantami ya bayar
da umarnin dakatar da wasu jami’an hukumar samar da rijistar
ƴan ƙasa NIMC, da ake zargi da karɓar wasu kudade daga
hannun mutane kafin su yi musu rijistar a ofisoshinsu na
Bauchi da kuma Kaduna.
A baya-bayan nan ne dai hukumar ta bayyana ɗaukar matakai
masu tsauri kan duk jami’an da aka kama da yin zagon kasa
ga shirin yi wa ‘yan kasar rijista, a yayin da ‘al’umma ke
ruguguwar ganin cewa sun yi samu shaidar zama ƴan ƙasar.
Ministan ya bayar da wannan umarni ne a wata sanarwa da ya
fitar, inda ya jaddada ɗaukar matakai masu tsauri kan duk
jami’in da aka kama da karɓar cin hanci da rashawa a yayin
gudanar da aikin rijistar shaidar zama ɗan kasa, da ya ce
tamkar yin zagon ƙasa ne.
A cikin shekarar da ta gabata ne Dr Isa Ali Pantami ya bayar da
umarnin cewa ƴan Najeriyar su tabbatar sun sada lambobin
wayarsu ta salula da kuma ta shaidar zama ɗan kasar, wanda
kuma sai wanda ya riga ya yi rijistar ɗan ƙasar ne zai iya
samun wannan lambar.
Wannan mataki in ji sanarwar ya biyo bayan wasu ƙorafe-
ƙorafe daga jama’a a jihohin Bauchi da Kaduna, a kan cewa
wasu daga cikin jami’an hukumar NIMC, na karɓar na goro
kafin su yi wa mutane rijistar, wacce tuni hukumomi suka riga
suka bayyana cewa kyauta ce.
Dole ne in ji wannan sanarwa, sai duk jami’an da aka ɗora wa
alhakin gudanar da aikin yi wa ƴan Najeriyar rijistar shaidar
zama ɗan ƙasar sun nuna dattaku da sanin ya kamata muddin
ana so a samu nasarar cimma burin da ake buƙata.
Mutane da dama a kasar na ta tururuwa zuwa cibiyoyin da aka
tanada domin yin wannan rijista a faɗin Najeriyar, inda galibi
ke kokawa da tsananin cunkoso da jinkiri wajen yin gudanar da
aikin domin samun lambar.
Ruguguwar dai ta biyo bayan umarni da kuma wa’adin da
hukumomin da suka bayar cewa duk wanda bai samu ya yi
rijistar da kuma sada lambar shaidar zama ɗan kasar da
wayoyin salularsa ba, za a rufe duka layukan nasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *