March 24, 2023

Ƙasashen Turai sun fi tallafa mana fiye da na Musulmai – Gwamna Zulum

2 min read
Share

Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya ce ƙasashen
Turawa sun fi taimaka wa jiharsa fiye da Larabawa Musulmi
yayin da suke fama da hare-haren ƙungiyoyin masu iƙirarin
jihadi.
Zulum ya bayyana hakan ne a jiya Talata yayin da yake karɓar
baƙuncin jakadan Falasɗinawa Saleh Fheied Saleh a Maiduguri,
babban birnin jihar.
“Ni mutum mai aiki da zahiri, tun bayan da muka shiga cikin
matsalolin nan, mun samu tallafi daga Birtaniya da sauran
sassan Turai da Amurka da Canada da Japan da sauran
waɗanda suka nuna damuwarsu garemu,” in ji gwamnan.
“Sai dai irin wannan tallafi bai taɓa zuwa daga ƙasashen
Larabawa ba, waɗanda muke addini ɗaya (Musulunci) da
kuma al’ada. Har Shuwa Arab muna da su a Borno, abin da ke
nuna yadda tarihinmu ke da alaƙa.
“Mun yi yunƙuri iri-iri, mun je ofisoshin jakadancin ƙasashen
Larabawa musamman masu arziki, amma da yawan ƙasashen
Larabawa ba su damu da halin da muke ciki ba kuma ba su ba
mu taimako ba.”
Gwamna Zulum ya kuma bayyana ziyarar jakadan da cewa mai
“ƙarfafa gwiwa” kuma ya gode masa.
A nasa ɓangaren, Ambasada Saleh Fheied ya bayyana cewa
akwai ‘yan asalin Jihar Borno a Falasɗin, ciki har da wata mai
suna Fatima Barnawi da ta taɓa zama minista kuma babbar
jami’ar ‘yar sanda.
“Akwai kamfanonin Falasɗinu da yawa a Najeriya da suke son
yin aiki tare da gwamnatin Borno kuma za mu yi duk abin da
kuke buƙatar mu yi domin taimakawa,” in ji jakadan.
Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar kashe mutum fiye da
36,000 a jihohin arewa maso gabashin Najeriya tare da jawo
asarar dukiya mai ɗumbin yawa cikin shekara fiye da 10.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Copyright © All rights reserved. | Newsphere by AF themes.