March 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ƴan sanda sun kama mutum 71 a gidajen rawa kan karya dokar hana yaɗuwar Covid-19

2 min read

Ƴan sanda a jihar Legas da ke Najeriya sun kai samame
wuraren rawa na dare da dama, inda suka kama mutum 71 kan
zarginsu da laifin take dokokin hana yaɗuwar Covid-19.
Ƴan sandan sun ce an kai samamen ne a unguwannin Lekki da
Surulere kuma za a tuhumi dukkan waɗanda ake zargin kan
laifin take dokokin da gwamnati ta sanya na daƙile yaɗuwar
cutar korona.
Mai magana da yawun ƴan sanda Olumuyiwa Adejobi, ya
shaida wa BBC cewa masu zuwa gidan rawar sun take dokar
nan da aka sanya ta haramta taruwar mutane da yawa da sake
buɗe gidajen rawa da kuma take dokar hana fita da daddare.
Hukumomi sun ce za su tsaurara kai samamen don tabbatar
da cewa an bi dukkan dokokin da aka sanya.
Kamen na zuwa ne a yayin da Najeriya ke ƙara samun
hauhawar masu kamuwa da cutar korona a kullum.
A ranar Litinin Hukumar Da ke Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa
ta NCDC, ta sanar da cewa san samu ƙarin mutum 1,204 da
suka kamu da cutar a ranar ɗaya, irin yawan da ba a taɓa
samu ba tun da cutar ta ɓulla.
A yanzu dai jumullar waɗanda suka kamu da cutar a ƙasar sun
kai 91,351 inda mutum 75,699 suka warke, sai kuma mutum
1,318 da suka mutu.
Jihar Legas ce cibiyar cutar a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *