March 24, 2023

Najeriya: Shin dokar dandaƙa ga masu fyade a jihar Kaduna na tasiri?

9 min read
Share

Matsalar fyade na ci gaba da kasancewa gagarumar matsala
a Najeriya inda kusan a kullum sai an samu labarin yin sa –
wasu lukutan kuma kan rutsa da kananan yara.
A watan Yunin shekarar da ta gabata illahirin gwamnonin
jihohin kasar 36 suka ayyana dokar ta-baci kan matsalar
fyaden, wadda ta kai ga wasu jihohi sun tsaurara dokokinsu na
yaki da fyade.
Ga alama dai jihar da ta fi daukar hankali ita ce jihar Kaduna da
ke arewacin kasar sakamakon dokar da gwamnatin jihar ta
kafa a watan Satumba ta dandaƙe duk wanda aka samu da
lafin yi wa yaro ko yarinya fyade da nufin dakile matsalar.
Ishaq Khalid ya duba lamarin:
‘Maza 10 sun yi wa ‘yar shekara 12 fyade’
Na tarar da mairainiya mai shekara goma sha biyu, Ladidi,
wanda ba ainihin sunanta kenan ba, tana zaune kusa da
babban wanta kuma mai kula da ita, tana ta zub da hawaye. Ta
yi gum, ta kasa fada mani abin da ya faru da ita watanni uku da
suka gabata.
Amma yayan nata ya yi mani bayani. Ya shaida mani cewa ana
zargin wasu maza goma ne suka yi mata fyade cikin watan
goma wato Oktoba – makwanni kalilan bayan da gwamnatin
jihar Kaduna ta ƙarfafa dokarta ta yaƙi da matsalar fyaɗe.
Sanadin lalatar, ta kamu da ciwon sanyi, ana kuma yi mata
magani. Danginta sun kadu, sun dugunzuma, suna kuma
dakon adalci ta fuskar shari’a. Mun dai sakaya sunansa domin
kada a shaida kanwar tasa.
Cikin takaici, ya ce lamarin ya yi matukar yi masu ciwo a zuci,
yana mai cewa ”sun cutar da rayuwar yarinya, kuma sun cutar
da mu.” Sai dai ya kara da cewa a kullum suna kokarin
rarrashinta da kuma karfafa mata gwiwa da cewa rayuwarta za
ta yi kyau a gaba.
An dai kama takwas daga cikin wadanda ake zargin – sauran
biyun sun gudu. Hukumomi na cewa duka za su fuskanci
shari’a.
Dan-uwan ”Ladidi” ya ce wasu daga cikin wadanda suka yi
mata fyaden mutane ne da kan yi hulda da gidansu, wannan
kuma na daya daga cikin abubuwan da suka girgiza su.
Katutun matsalar ƙyama da tsangawama ga wadanda aka yi
lalata da su, da karancin kai rahoton fyade ga hukumomi, da
karancin hukunta masu fyaden da kuma jinkiri da sarƙaƙiya ta
fuskar tsarin shari’a na daga cikin kalubalen da ake fuskanta
wajen daƙile matsalar fyade a Najeriya, a cewar masu sharhi.
Amma yayan Ladidi ya ce fatansu shi ne kotu ta samu
wadanda ake zargi da yin lalata da ƙanwarsa da laifi, kuma a
hukunta su daidai da sabuwar dokar yaƙi da fyaɗe ta jihar
Kaduna – wato a dandaƙe su kuma a zattar masu da hukuncin
kisa.
Matsalar fyade ta zama annoba
Kusan a kullum dai sai an samu labarin cewa an yi wa wata ko
wani fyaɗe a Najeriya. Kungiyoyi, musamman masu fafutikar
kare hakkin mata da kananan yara, na ta yin kumaji da kuma
nuna damuwa kan matsalar ta fyade – matsalar da wasu ke
cewa ta zama annoba a cikin al’umar kasar.
Ko a cikin shekarar da ta gabata irin wadannan kungiyoyi sun yi
ta yin zanga-zanga a tituna a sassa daban-daban na Najeriya
domin kara jawo hankalin al’uma da mahukunta ga matsalar.
Yayin da yake da wahala a iya samun takamaiman alkaluma
na hakikannin yawan fyade a Najeriya mai jihohi 36, a jihar
Kaduna kadai hukumomi sun ce an samu rahotannin lamuran
fyade 1,046 daga watan Janairu zuwa watan Nuwamban 2020.
Wannan adadi na nuni da karuwar kamar kashi 50 cikin 100
kan yawan fyade da aka samu rahotanninsu a 2019 a jihar.
Duk da haka an yi imanin cewa akwai lamuran fyade da dama
wadanda ba a kai rahotanninsu ga hukumomi ba. Haka zalika
ba kasafai ake hukunta masu fyaɗe a kotuna ba.
Wasu kuma cewa su ke yi kamata ya yi a maida hankali ga
shawo kan matsalolin dake janyo fyade baya ga kokarin
hukunta masu aikatawa.
Hajiya Rabi Salisu Ibrahim wata mai fafutikar yaki da fyade ce.
Kungiyarta mai suna Arida Relief Foundation ta bi diddigin
lamuran fyade fiye da 500 cikin shekaru biyar da suka gabata –
to amma bakwai ne kacal suka kai ga samun hukuncin kotu
kan wadanda aka gurfanar.
Ta ce matsalar ba ta sauya doka ko kafa sabuwar doka ba ce,
a ‘a, ana bukatar daukar karin matakai ne na zahiri wajen
aiwatar da dokokin, da kuma ingantawa da hanzarta tsarin
gabatar da shaida ko kuma hujjar tabbatar da fyade. Hajiya
Rabi ta koka da wahalar da ake fuskanta wajen gabatar da
shaida da kuma dawainiya tsakanin hukumomin tsaro da
asibiti.
Ta shaida wa BBC cewa wasu daga cikin hujjoji da ake bukata
sun hada da tabbatar da cewa lallai akwai saduwa a tsakani,
ko alamar rauni ko kuma jini daga wanda ake zargin an yi wa
fyade. Mai fafutikar ta ce wannan babban kalubale ne wajen
tabbatar da laifi a kotu.
Ta kuma ce sarkakiyar shari’a kan sa wani lokaci shari’ar fyade
ta iya daukar ”shekaru 10” ana yi, kuma irin wannan yanayi kan
sanyaya gwiwar wadanda aka yi wa fyade ko kuma iyayensu,
har su gaji su ce sun janye daga shari’ar.
Ba a hukunta kowa ba tun bayan kafa dokar dandaka a jihar
Kaduna.
Dokar ta jihar Kaduna tana janyo cece-ku-ce musamman batun
tanadin hukuncin dandaka ko cire bututun mahiafa da kuma
kisa ga wanda ya yi ko ta yi fyade ga yaro ko yarinyar da ba su
wuce shekara 14 da haihuwa ba.
Labarai masu alaƙa
Dokar ta kuma tanadi hukuncin dandaka da kuma daurin rai-
da-rai idan wadda aka yi wa fyaden ta wuce ko ya wuce
shekara 14 da haihuwa.
Amma daya daga cikin hujjoji da ake bukata shi ne sakamakon
gwaji na asibitin gwamnati dake tabbatar da cewa an yi lalata
da yaron ko yarinyar. A watan Satumban 2020 ne gwamnan
jihar Malam Nasir el-Rufai ya sanya hannu a kan dokar bayan
da majalisar dokokin jihar ta amince da ita.
Gwamnatin jihar Kaduna dai ta ce ta kafa dokar ne domin ta
kasance ishara ko izina ga masu aikata fyade a jihar saboda
yadda fyade ta yi yawa musamman ga kananan yara. Dokar ta
sha yabo daga masu fafutikar yaki da fyade inda wasu suka yi
fatan zata tsorata masu fyade – musamman idan aka aiwatar
da hukunci.
Haka nan mutane da dama sun ce kafa dokar ya taimaka
wajen kara bayyana girman matsalar fyade da kuma bukatar
daukar mataki.
Amma wasu na ganin ba a nan gizo ke saka ba. Kwamishinar
kare hakkin bil-Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Michelle
Barchellete, ta ce akwai mugunta cikin dokar, kuma tamkar
neman magance ɓarna ce da wata ɓarnar. Ta kara da cewa
dokar ta keta hakkin-Adama.
To sai dai tun da dokar ta jihar Kaduna ta soma aiki cikin
watan Satumba, kawo yanzu, kotu bata samu wani da laifin
fyade bisa tanade-tanaden dokar ba, balle a yi batun dandake
shi ko hukuncin kisa, ko kuma cire bututun mahaifa.
Haka kuma kawo yanzu babu alamar adadin fyade da ake yi a
jihar ya ragu bayan kafa dokar.
Hafsat Baba ta ce jihar Kaduna na kan kyakkyawar turbar
magance fyade
To amma kwamishinar Ayyukan Kyautata Rayuwar bil-Adama
da Zamantkewa ta Jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba, ta ce ya
yi wuri a yanke hukunci kan tasiri da ingancin dokar –
kasancewar watannni kalilan ke nan da aka kafa ta.
Hajiya Hafsat Baba ta shaida wa BBC cewa lallai jihar Kaduna
ta na kan kyakkyawar turba ta magance matsalar fyade kuma
a cewarta, mutane na farin ciki da dokar.
Kwamishinar ta jihar Kaduna ta ce shari’a na da tsarinta kuma
dole a bi tsarin kafin a kai ga yanke hukunci da kuma zattas da
hukunci.
Ta bayar da tabacin cewa da yardar Allah za a aiwatar da
dokar a kan duk wanda aka samu da laifi, kuma yanzu
hukumomi na tsare-tsaren yadda za a rika hanzarta yin
shari’o’in fyade a jihar.
Dangane da zargin da wasu ke yi na cewa dokar ta yi tsanani
kuwa, jami’ar ta ce ”Da wannan doka ta fito, masu korafi a
kanta, sai muka ga kamar sun fi tausaya wa wanda ya yi fyade,
fiye da wanda aka yi wa fyaden, ko namiji ne ko tamace.”
Ta kara da cewa akwai bukatar kare hakkin wadanda aka yi wa
fyade domin duk wanda aka yi wa fyade an yi wa rayuwarsa
illa kuma ”hatta iyaye da ‘yan-uwansa” za su shiga ”wani hali.”
Sai dai masu fafutika irinsu Hajiya Rabi Ibrahim na nuna bacin
ransu kan rashin hukunci tun bayan kafa dokar ta jihar Kaduna.
Ta bayyana fargabar cewa muddin ba a yin hukunci, to za a ci
gaba da fuskantar ayyukan fyade a cikin al’uma.
Wani batu da hukumomi da kuma masu fafutika ke kokawa a
kai shi ne yadda masu unguwa ko kuma ‘yan uwan yaran da
aka yi wa fyade kan yi kokarin sasanta matsalar a gida ba tare
da an kai ga hukuma ba – wasu lokutan da sunan cewa
matsala ce ta cikin gida da kuma gudun ”abin kunya” idan
maganar da fita waje.
A wasu lokuta kuma ana zargin amfani da kudi wajen kashe
wutar maganar musamman idan wanda aka zalunta mai
karamin karfi ne.
Amma jihohi da dama na sauya dokokinsu domin mayar da
laifin fyade ya kasance babban laifi wanda ko iyaye da ‘yan
uwa sun janye daga maganar, gwamnati na da hakkin bin kadin
wanda aka yi wa fyade da kuma hukunta wanda ya aikata.
Jihar Kaduna na cikin irin wadannan jihohi.
Yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ku ce kan tasirin dokar ta
fyade a jihar Kaduna, su kuwa wadanda aka yi wa fyade kamar
marainiya ”Ladidi”, da danginsu, na fatan watan wata-rana za a
yi masu adalci, a hukunta wadanda aka samu da laifin
zaluntarsu.
Wadanda aka yi wa fyade na bukatar
kulawa
Yayan marainiya ‘yar shekara 12 da ake zargin an yi mata
fyade wato ”Ladidi” ya ce tun bayan faruwar lamarin ba ta da
sukuni a rayuwarta.
Ya ce kafin faruwar lamarin, Ladidi yarinya ce mai kazar-kazar
da walwala, amma yanzu ”sai ka same ta ta zauna ta yi shiru
tana da tunani” kuma ba ta cika shiga cikin sauran yara tana
wasa kamar yadda ta saba ba.
Masana na bayyana irin wannan yanayi a matsayin daya daga
cikin manyan alamomi na tsananin damuwa a rayuwa da kan
shafi tunani da kwakwalwar mutum.
Wata kwararriya kan tunani da halayyar bil-Adama, Dakta
Fatima Akilu, ta shaida wa BBC cewa yayin da hukumomi ke ta
kokarin kafa dokoki da kuma hukunta masu aikata fyade, yana
da muhimmanci a mayar da hankali wajen taimaka wa
wadanda aka yi wa fyade ta fuskar gyara rayuwarsu da kuma
tunaninsu.
Ta ce ”wadanda aka yi wa fyade na bukatar taimako” saboda
fyade kan gigita rayuwar duk wanda aka yi wa – imma namiji
ko ta mace. Ya kamata a kafa cibiyoyin bai wa wadanda aka yi
wa fyade shawarwarin kwararru a Najeriya, inji Dokta Fatima.
Kwamishinar Ayyukan Kyautata Rayuwar bil-Adama da
Zamantakewa ta jihar Kaduna Hajiya Hafsat Baba ta ce yanzu
haka akwai cibiyoyi hudu na kula da wadanda aka ci zarafinsu
a jihar Kaduna inda ake yin gwaje-gwajen likita, da ba su
taimako ta fuskar lafiya da kuma shawarwarin kwararru ta
fuskar tunani da kuma rarrashi.
A bangare guda kwararriya Dr Fatima Akilu ta ce dole ne a
kara horar da alkalai da lauyoyi da kuma masu fafutika kan
yadda za a inganta tattaro hujjoji da shaidu ta hanyar kimiya
domin a samu nasara idan aka kai kara a kotu kan matsalar
fyade.
Sai dai ta ce ko da yake yin hukunci ga wadanda suka aikata
fyade na da matukar muhimmanci wajen magance matsalar a
cikin al’umma, amma hukunci ba shi ne kadai matakin
magance matsalar fyade ba, sai an hada da daukar wasu
matakan.
Mutane da dama na kallon cewa neman biyan bukatar jima’i ne
ke ingiza wasu su aikata fyade, amma wasu masu sharhi na
cewa ba sha’awar jima’i ce kadai ke sa wasu aikata fyade ba.
Akwai wasu dalilan da suka shafi tunaninsu da kwakwalwarsu,
imma neman huce wani haushi ko kuma wani dalilin na daban
kamar tsafi.
Dokta Fatima ta ce mai da himma wajen yin nazari kan dalilan
da kan sa mutane su aikata fyade, shi ma yana da
muhimmanci da nufin dakile su musamman ganin yadda a
cewarta yanzu matsalar fyade ”ta yi katutu cikin al’umma.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Copyright © All rights reserved. | Newsphere by AF themes.