April 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Najeriya: Yawan rundunonin soja da ke yaƙi da ƴan bindiga

3 min read

Yawan rundunonin soji da ke yaƙi da masu ɗauke da makamai
a Najeriya ya nuna girman matsalar tsaro a ƙasar.
Najeriya ta shafe shekaru tana fama da rikicin Boko Haram a
arewa maso gabashi da matsalar ƴan bindiga masu fashin daji
da satar mutane a arewa maso yammaci da arewa ta tsakiya.
Akwai kuma matsalar masu fasa bututu a kudancin ƙasar
musamman yankin kudu maso kudu.
Girman matsalolin tsaron a sassan ƙasar ya raba rundunar
sojin Najeriya, inda ta kafa rundunoni a yankunan ƙasar domin
kawo ƙarshen matsalolin.
Dubban mutane aka kashe tare da raba miliyoya da gidajensu a
hare-haren Boko Haram da ƴan bindiga masu satar mutane a
arewacin Najeriya.
Tun kafin hawan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ɗaya
daga cikin manyan alƙawura uku da ya yi shi ne na kawo
ƙarshen matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa musamman a
arewa maso gabashin ƙasar.
Ko da yake gwamnatin Buhari ta APC na cewa tana iya
ƙoƙarinta na kawo ƙarshen matsalolin tsaron musamman a
yankin arewacin ƙasar.
Yawan rundunonin soji
Arewa Maso Gabas
A Kwanan nan rundunar sojin Najeriya ta kafa sabuwar
rundunar Operation TURA TAKAIBANGO a yankin arewa maso
gabashi domin kakkabe mayaƙan Boko Haram
Rundunonin Operation Lafiya Dole da kuma Operation Hail
Storm sun da daɗe suna yaƙi da ‘yan ƙungiyar Boko Haram da
kuma na ISWAP a arewa maso gabashin Najeriya.
Operation Lafiya Dole runduna ce ta sojin ƙasa da ke faɗa da
Boko Haram inda kuma take samun taimako daga rundunar
Operation Hail Storm da ke kai hare-hare ta sama.
Arewa Maso Yamma
A arewa maso yammacin Najeriya, akwai Rundunonin
Operation Hadarin Daji da kuma Operation Sahel Sanity.
An kafa rundunonin ne a yankin musamman jihohin Zamfara da
Katsina da Kaduna domin yaƙi da ƴan bindiga masu fashin daji
da satar mutane domin kuɗin fansa da kuma satar shanu.
Aikin rundunonin ya shafi yaki da ƴan bindiga da suka addabi
yankin arewa maso yammacin Najeriya, inda satar mutane ta
zama ruwan dare.
Arewa Ta Tsakiya
A arewa ta tsakiya, akwai rundunonin Operation Safe Haven da
Operation Thunder Strike da Operation Whirl Stroke da ke yaƙi
ƴan bindiga da ɓarayi a yankin.
Aikin rundunonin ya shafi kai hare-hare ta ƙasa da kuma sama.
Shin kwaliyya tana biyan kuɗin sabulu?
Watanni kaɗan bayan da Shugaba Buhari ya hau kan karagar
mulki a 2015, mutanen ƙasar musamman na arewa maso
gabashi suka fara shewa da nuna jin daɗinsu sakamakon ganin
alamun kwaliyya ta fara biyan kuɗin sabulu, ganin cewa an
ɗauki tsawon lokaci babu tashin bama-bamai, da kuma
shingaye kan hanya da aka cire.
An kuma daina samun tashin bama-bamai a jihohin Kaduna da
Kano da Filato da sauran jihohin arewa maso yammacin ƙasar.
Wannan dalili ne ya sa wasu ‘yan ƙasar ke ganin kamar
shugaban ya kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar.
Amma shekaru kaɗan bayan hakan, wasu ‘yan ƙasar da
ƙungiyoyi masu zaman kansu suka fara kiran gwara jiya da yau,
sakamakon yadda matsalar tsaron ke ƙara ƙamari a faɗin
ƙasar.
Satar ɗaliban makarantar sakandaren Kankara a jihar Katsina a
watan Disamba kafin a kuɓutar da su ya tayar da hankali a
Najeriya tare da kara fito da girman matsalar tsaro a ƙasar
A kwanakin baya, ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International
ta bayar da rahoton cewa an kashe kimanin mutum 1,126 a
jihohin arewacin Najeriya tsakanin watan Janairu zuwa Yuni.
A kwanakin baya ma sai da wani uban ƙasa a jihar Katsina ya
shaida wa bustandaily cewa ‘yan bindiga sun mayar da mata 600
zawarawa a yankin Batsari da kuma mayar da yara sama da
2,000 marayu.
Wasu na ganin irin yawan rundunonin da aka kafa a arewacin
ƙasar, ya kamata a ce an kawo ƙarshen matsalar tsaro a
yankin.
Ko da yake sojojin cewa suna samun nasarori a yakin da suke
yi da ƴan bindiga
An ruwaito cewa sama da mutum 3,000 aka kashe a jihar
Zamfara tun daga 2011 tare da garkuwa da sama da mutum
500.
Ita ma ƙungiyar nan mai bincike kan tashe-tashen hankula a
kasashen duniya, International Crisis Group, ta ce an kashe
mutane fiye da dubu takwas a rikicin arewa maso yammacin
Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *