March 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Tsaro: Yadda aka yi garkuwa da mutum 30 a Birnin Gwari

2 min read

Rahotanni daga jihar kaduna da ke arewacin Najeriya na nuna
cewa an kai hari ƙauyen Kungi da ke yankin Birnin Gwari da
safiyar yau Alhamis.
Ana tunanin an yi awon gaba da mutane sama da 30 a harin
sannan mutum ɗaya ya rasa ransa.
Har yanzu hukumomin jihar Kaduna ba su ce komai ba
dangane da wannan harin.
Sai dai wani mazunin ƙauyen wanda bai amince a ambaci
sunasa ba ya shaida wa BBC cewa “maharan sun faɗa cikin
gidan mutane su kara wa mutum bindiga, sai su ce mu tafi,” a
cewarsa.
Ya ce mutumin da aka kashe ya yi wa maharan gardama ne, ya
nuna masu ba zai bi su ba shi ya sa suka harbe shi.
Ganau din ya bayyana cewa cikin wadanda aka sace akwai
maza da mata har ma da ƙananan yara. Ya ce har da jikokinsa
guda uku a cikin mutanen.
“Ɗiyata ce ta haife su, su ma suna cikin mutanen da aka tafi da
su” kamar yadda ya bayyana.
Ya bayyana cewa garin Kungi na nan a cikin zaman ɗar-ɗar
saboda abin da ya faru.
“Muna cikin wani hali a yankin Birnin Gwari. Mun miƙa komai
wurin Allah saboda tashin hankalin ya ishe mu. Bala’i ya kai
bala’i,” in ji shi.
Sai dai ya ce akwai jami’an tsaro da dama a gaba ɗaya yankin
na Birnin Gwari amma zaman su bai hana ayyukan masu
garkuwa da mutane ba.
Mutumin ya ce ko da maharan suka shigo garin sun yi tunanin
sojoji ne saboda irin bindigogin da suka riƙe, sai daga baya
suka fahimci ashe ƴan bindiga ne.
Ya ce su yanzu kawai sun sa wa ransu Allah ne ke kare su.
Ya bayyana cewa a halin yanzu Garin Birnin Gwari na cike da
ƴan gudun hijira manya da yara daga ƙauyuka da ke yankin
saboda zaman ƙauyen ya gagare su.
Yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari ya daɗe a halin rashin
tsaro na hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane
don neman kuɗin fansa.
Dubban mutane ne ke tserewa daga kauyuka daban-daban na
yankunan kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari inda
suke neman mafaka a garin Buruku na jihar Kaduna a arewacin
Najeriya.
A hare-haren da ‘yan bindiga ke kai musu a ‘yan kwanakin nan,
al’amarin ya yi sandin asarar rayuka da raunata mutane da
dama, baya ga awon gaba da ake zargin maharan sun yi da
mutane da kayayyaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *