March 29, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Zagin sahabban Annabi -Dr Bashi ba sulhu muke so ba hukuncin Shari’a mukeso

1 min read

Limamin Masallacin Juma’a na Alfurkan dake nasarawa a nan kano Dakta Bashir Aliyu ya bukaci Gwamnati data zartar da hukuncin Shari’a akan Abduljabbar Nasir kabara bisa kamashi da kalaman batanci dazagin sahabban Annabi Muhammad SAW da halinsa baki daya.

Dakta Bashir ya ce Abduljabbar ya dade yana gudanar da irin wadannan Abubuwa Wanda hakan ya sabawa shari’ar musulunci.

Ya kuma ce lallai ne gwamnati ta Sanya Ido akan irin wadannan Abubuwa da suke neman zamarwa Jihar kano kalubale domin kuwa hakkin duk wani musulmi ne ya Kare Martabar janibin Annabi Muhammmad SAW.

Malamin ya kuma godewa gwamnatin Jihar Kano bisa kokarinta na dakatar da Masallaci Abduljabbar da kuma hanashi gudanar da tafsirai a fadin Jihar Kano baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *