March 29, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ya kamata Matasa su dage wajen neman ilimin kimiyya da fasaha

1 min read

Daraktan kungiyar Arewa Agenda dake nan Kano Alhaji Muhammmad Dahiru Lawan ya bukaci Matasa dasu dage wajen neman ilimin fasahar zamani domin samun sana’o’in dogaro Alhaji Muhammmad Dahiru Lawan ya bayyana haka ne a yayin taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a nan Kano.

Daraktan ya Kuma ce matasan Jihar suna da karancin ilimin fasahar zamani,inda ya ce akwai abubuwa masu yawa dake kawo kudi a fannin fasahar zamani.

Alhaji Muhammmad Dahiru Lawan ya ce arewacin kasar nan an barsu a baya a bangaren fasahar zamani, musamman idan aka duba irin cigaba da kudancin Nigeria ya sami a halin yanzu.

Jaridar Bustandaily ta ruwaito cewa kungiyar ta bukaci kafafan yada labarai dana internet dasu wayar da Kan marasa hanyoyin da ya kamata su bi wajen bunkasa fasahar zami.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *