March 28, 2023

An sace mutane 12 ‘yan Kano a Kaduna By Bilal Nasidi Mu’azu

2 min read
Share

Masu garkuwa da mutane sun sace mutane goma sha biyu ‘yan gida daya, kuma ‘yan asalin jihar Kano a karamar hukumar birnin Gwari dake jihar Kaduna.

Bustandaily ta ruwaito cewa iyalan, dukkaninsu mazauna unguwar Garu ne dake karamar hukumar Kumbotso a nan Kano.

Rahotannin sunce an sace su ne a hanyarsu ta dawowa Kano, bayan da suka halarci biki a jihar Neja.

Kimanin kwanaki takwas kenan da sa ce su, amma har yanzu basu samu ‘yanci ba.

Wani da matarsa da ‘ya’yan sa biyu ke cikin wadanda akayi garkuwa dasu, Shehu Yahya ya ce masu garkuwa da mutanen sun bukaci da su biya naira miliyan saba’in.

Sai dai ya ce daga baya sun rage zuwa naira miliyan goma, inda suka ce daga wannan ba za su kara rage ko sisi ba.

Ya ce wadanda aka sace sun hada da Safiya Shehu mai shekaru 60, sai Asma’u Yahya ‘yar shekara 75, da Hadiza Abdullahi mai shekara 90, da Talatu Abdullahi ‘yar shekara 85 ,da kuma Habiba Auwalu mai shekara 35.

Sauran sune Habiba Auwalu, da Fatima Ali, da Khadija Usman, sai Saifullahi Usman, da Khadija Abdullahi, sai Hamisu Adamu, da kuma direban motar mai suna Abubakar Na’ibawa.

Ya kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun kira su a waya, inda suka ce sun kashe mutum guda a cikin mutane goma sha biyu a don haka a biya kudin fansa a dauki gawar sa.

“Mata goma ne cikin wadanda suka kama ma za biyu, to yanzu sunce sun kashe mutum guda daga cikin su.

“Kullum sai sun kira mu a waya sun saka mana kukan su da yadda suke nada musu na jaki, muna rokon hukuma da ta shiga lamarin,” a cewar sa.

Hamisu Garu, ya ce sun sanarwa da rundunar ‘yan sanda ta kasa da gwamnatin jihar Kaduna amma har yanzu ba a kubutar dasu ba.

Ya ce mahaifiyyarsa da kannen sa guda biyu duk suna hannun masu garkuwa da mutanen kuma babu wanda aka saka a cikin su.

Sai dai da muka tuntubi runduanr ‘yan sandan jihar Kano kan al’amarin ta ce bata da hurumi a kai.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ce ke da hurumi kan al’amarin.

Haka zalika da aka tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar ta Kaduna ta ce za ta bincike al’marin.

Mai Magana da yawun rundunar Muhammad Jalige ya ce da zarar sun kammala bincike za su sanar da mu halin da suke ciki

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Copyright © All rights reserved. | Newsphere by AF themes.