March 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hisba-Gasar sarauniyar kyau Haramun ce

2 min read

Hukumar Hisbah ta jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce haramun ne yin gasar sarauniyar kyau.

Shugaban hukumar, Sheikh Muhammad Harun Ibn-Sina, wanda ya bayyana hakan a wata hira da Bustandaily ya ce yin gasar sarauniyar kyau wani nau’i ne na koya wa mata rashin kunya.

Yana bayani ne kwanaki kadan bayan wata matashiya ‘yar jihar Kano, Shatu Garko, ta lashe gasar sarauniyar kyau.

Shatu, mai shekara 18, ta doke zaratan mata 18 a bikin da aka gudanar ranar Juma’a da dare a Landmark Centre da ke birnin Legas.

Ita ce mace ta farko mai hijabi da ta lashe gasar a tarihi kuma wannan ne karo na 44 na gasar wadda ake kira Miss Nigeria a Turance.

Nicole Ikot ce ta zo ta biyu, sai kuma Kasarachi Okoro da ta zo ta uku.

‘Keta alfarmar Musulunci’

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?
Korona: Ina Mafita?
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi
End of Podcast
Ibn Sina ya ce “maganar shiga takarar gasar sarauniyar kyau haramun ne…saboda na farko, ana keta alfarmar musulunci a ciki. Sannan ana bayyana al’aura a ciki, ana karfafa gwiwar ‘ya’ya mata su fito ba tare da kunya ba, wato a koya musu rashin kunya”.

Ya ambato wata ayar AlKur’ani mai tsarki da wani bangarenta yake cewa bai kamata mace ta nuna kwalliyarta ba “sai abin da ya bayyana.”

“Sannan su sa mayafi su rufe jikinsu gaba daya, kuma kada su bayyana kwalliyarsu sai ga mazansu ko iyayensu ko ‘ya’yansu… wannan yana nuna cewa illa ce ga ‘ya mace a matsayinta na mumina ta yi irin wannan [gasa],” a cewar Ibn Sina.

Sai dai wasu ‘yan Najeriya suna sukar hukumar ta Hisbah bisa mayar da hankali kan mutane marasa karfi a yayin da take ikirarin tabbatar da tarbiyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *