March 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mun yaba ga ayyukan Sanata Barau Jibril Kano ta Barau ce 2023

1 min read

Kungiyar Daliban Kano ta Arewa ta jaddada goyon bayanta ga sanatan Kano ta Arewa Sanata Barau jibril bisa irin ayyukan cigaba da ya ke samarwa a ga al’ummar Kano ta Arewa gama Kasa baki daya.
Shugaban kungiyar kwamared Yahaya Hamisu Rimin Gado ne ya bayyana haka a yayin zantawar sa da manema labarai a daren jiya Talata kan wasu kalamai da wasu marasa kishi keyi akan sanatan.

Kwamared Yahaya ya kuma ce Dalibai da sauran al’umma na cigaba da amfana da irin manyan ayyuka da taimako al’umma ta ko wani bangare da ya ke gudanarwa wanda baza’a taba butil ceea wannan kokari nasa ba.

Ya ce ya samar musu da da tallafin karatu noma ayyuka daukar ayyuka raba mota da bubura jari ga mata da dai sauransu.

Kungiyar dalibai ta kuma bukaci sanatan Kano ta Arewa da yayi musu alfarmar tsayawa takarar kujerar Gwamnan Kano ta zaben shekara ta 2023 mai zuwa.

Jaridar Bustandaily ta ruwaito cewa kungiyar daliban ta yabawa sanatan Kano ta Arewa bisa kokarinsa na tallafawa cigaban dalibai da matasan yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *