March 29, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rikicin APC a Kano: Fadar shugaban Najeriya ta ce Buhari bai taya wani bangare murna ba

2 min read

Fadar gwamnatin Najeriya ta musanta bayanan da ke cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya taya murna ga shugaban jam’iyar APC na jihar Kano bangaren Sanata Ibrahim Shekarau.

Sanarwar da mai bai wa Shugaban shawara kan yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar ta ce “batun ba gaskiya ba ne, ba zai taba yiwuwa shugaban ya yi haka ba alhali ana jiran hukunci daga kotu.”

Sanarwar ta kara da cewa babu wani bangare na jam’iyar APC a Kano da Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna wa goyon baya.

A cewar Malam Garba Shehu “goyon bayan Shugaban na jam’iyar APC ne kacokan, kuma fatansa shi ne ta kara zama tsintsiya madaurinki daya, ta hanyar kawar da bangaranci a cikinta.”

Tunda farko Alhaji Ahmadu Haruna Zago, wanda bangaren tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Ibrahim Shekarau ya zaba a matsayin shugaban jam’iyyar ya fada wa BBC cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya shi murnar zamansa shugaban jam’iyyar APC a Kano, yayin wata tattaunawa da suka yi a fadar shugaban a Abuja.

Kuma ganawar na zuwa yayin da ake ci gaba da rikici kan shugabancin APC reshen jihar ta Kano tsakaninsa da Abdullahi Abbas na bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

A zaman kotu da aka yi a baya, alkali ya jaddada sahihancin shugabancin APC bangaren da Zago ke jagoranta, wanda hakan ya sa bangaren Gwamna Ganduje daukaka kara.

Tun farko tirka-tirka tsakanin bangarorin biyu ta samo asali ne bayan Sanata Shekarau da wasu ‘yan majalisar dokokin tarayya sun balle daga bangaren Gwamna Ganduje, inda suka zarge shi da rashin iya shugabanci.

Hakan ya sa bangarorin biyu kowa ya gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar.

Amma kuma a tattaunawar da Ahmadu Zagon ya yi da Shugaba Buhari, ya ce ba su tabo batun rikicin da ya dabaibaye jam’iyar ba a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *