April 25, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ana zargin Yan shi’a da yunkurin kone wani masallaci a Unguwar Doraryi Babba

1 min read

Rohotanni daga Unguwar Doraryi Babba dake cikin karamar hukumar Gwale na nuni da cewa Yan shi’a sun kone wani masallaci a Unguwar.

Shaidun gani da Ido sun tabbatar da cewa da tsakar Daren Alhamis ne Yan shi’a dauke da da adduna suka kutsa cikin masallacin a yayin da al’ummar yankin ke kwance a gidajensu.


Wani Malam Ahmad Dauda ya shaidawa wakilin Bustandaily cewa dama yan shi’ar sun dade da Sanar da cewa zasu kone masallacin tare da kashe Mai Unguwar yankin da Kuma liman Malam Saminu.

Rikici tsakanin Yan shi’a da al’ummar yankin ba sabon Abu bane a yankin Dorayi Babba.

Mun yi kokarin ji daga Bakin rundunar Yan sanda Kano a tabakin kakakinta ya ce zasu bincika domin Sanar da manema labarai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *