September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Cikekken bayani Kan umarnin Kotun Daukaka Kara ta Najeriya Kan komawar ASUU bakin aiki

2 min read

Kotun Daukaka kara ta Najeriya ta umarci kungiyar malaman jami’o’i ta kasar, ASUU da ta gaggauta komawa bakin aiki ba tare da bata wani lokaci ba.

Hukuncin ya biyo bayan daukaka karar da kungiyar ta yi ne a kan hukuncin da Kotun Kwadago ta kasar ta yi ne inda ta umarci kungiyar ta ASSU da ta kawo karshen yajin aikin da ta kwashe wata takwas tana yi.

Sakamakon kasa warware dambarwar da ke tsakanin bangarorin biyu ne, gwamnatin Najeriya ta gurfanar da kungiyar malaman jami’o’in a gaban Kotun Kwadagon.

Daga nan ne ita kuma Kotun Kwadagon a ranar 21 ga watan Satumba ta umarci kungiyar da ta koma bakin aiki ba tare da bata wani lokaci ba, kafin a kai ga warware sabanin da ke tsakaninsu da gwamnati.

Kotun daukaka karar ta shawarci bangarorin biyu da su je su sasanta rikicin a wajen kotu, amma kuma abin da ya ki yuwuwa, kamar yadda babban lauyan da ke wakiltar ASUU Femi Falana (SAN), ya sheda wa kotun yayin zamanta a Abuja, a jiya Alhamis.

Haka shi ma lauyan bangaren gwamnati a shari’ar James Igwe ya shaida wa kotun cewa sasanton a waje ya gagara.

A hukuncin da ya yanke yau Juma’a alkalin Kotun Daukaka Karar Justice Hamman Barka ya umarci kungiyar malaman da ta koma aiki ba tare da wani bata lokaci ba.

Ita dai ASUU tana yajin aiki tun ranar 14 ga watan Fabrairu, inda mambobinta wato malaman jami’o’in gwamnati suka dakatar da aiki a kan kin biyansu kudaden alawus-alawus tare da neman kyautata jin dadinsu da sauran bukatu daga gwamnatin tarayya.

Gwamatin Najeriya ta yi wa wasu sabbin kungiyoyi biyu na malaman jami’a da suka bullo wadanda ke zaman tamkar kishiya ga ASUU.

Kungiyoyi su ne CONUA da NAMDA ( Congress of Nigerian Universities Academics) da (National Association of Medical and Dental Academics).

Kuma ASUU ta ce za ta kai gwamnati kara kan yi wa kungiyoyin biyu rijista.

,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *