Kungiyar Asuu Nazarin hukuncin Kotun Daukaka Kara, mu Sanar da mataki na gaba
2 min read
Nafisa Abubakar
Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta ce za ta yi nazari kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke wa kungiyar ta dakatar da yajin aikin da ta yi, domin sanin matakin da za ta dauka na gaba.
Kotun daukaka kara a yau Juma’a ta umurci kungiyar da ta koma bakin aiki kamar yadda kotun masana’antu ta kasa ta ba da umarnin fara aiki nan take.
Da yake mayar da martani kan sabon hukuncin da kotun ta yanke, Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya shaida wa manema labarai cewa kungiyar har yanzu ba ta karbi hukuncin kotun daukaka kara ba a hukumance.
Talla
Ya ce kungiyar bayan ta samu hukuncin za ta bi takardar tare da lauyoyinta sannan ta yanke hukunci kan matakin da za ta dauka na gaba.
Ya ce, “Ba mu samu hukuncin ba, idan muka samu za mu duba shi da lauyanmu sannan mu dauki mataki na gaba”.
A tuna cewa gwamnatin tarayya bayan gaza cimma matsaya da malamin jami’ar, ta kai kungiyar ASUU gaban kotun masana’antu ta kasa a ranar 11 ga watan Satumba.
Kotun a ranar 24 ga watan Satumba ta umurci malaman da ke yajin aikin da su koma aji yayin da ake ci gaba da tattaunawa da gwamnatin tarayya.
Sakamakon rashin amincewa da hukuncin, kungiyar ta garzaya kotun daukaka kara domin daukaka kara kan hukuncin.
WhatsAppFacebookTwitterTelegramShare