July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An tsinci gawar mutum biyar ‘yan gida ɗaya

1 min read

Mazauna ƙauyen Amutenyi da ke Ƙaramar Hukumar Udenu ta Jihar Enugun Najeriya sun wayi gari da tashin hankali sakamakon mutuwar mutum biyar ‘yan gida ɗaya a gidansu.

Lamarin ya faru ranar Asabar, wanda ya haɗa da wata mace da ‘ya’yanta biyu da ‘yan uwanta mata biyu da suka kai mata ziyara, a cewar rahotanni.

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar ta ce an kai gawar mutanen mutuware don gudanar da bincike game da abin da ya yi ajalinsu.

Kakakin rundunar, Daniel Ndukwe, ya ce an rabu da mutanen lafiya ƙalau da dare amma sai gawarsu aka gani da safe a ɗaki biyu daban-daban.

Ya bayyana sunayensu da: Chinyere Odoh, da ‘ya’yanta biyu – Udochukwu Odoh (mace mai shekara bakwai) da Chukwuemeka Odoh (namiji mai shekara huɗu). Sai kuma ‘yan uwanta Martina Ezeme da Ngozi Ezeme.

Ya ƙara da cewa Kwamashinan ‘Yan Sanda Ahmed Ammani ya ba da umarnin ƙaddamar da bincike nan take.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *