June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Manyan Motoci Sun Tare Hanyar Abuja Kan Rufe Masana’antar Dangote

2 min read

Manyan Motoci Sun Tare Hanyar Abuja Kan Rufe Masana’antar Dangote

Direbobin manyan motoci sun tare babbar hanyar Lakwaja zuwa Abuja domin nuna fushinsu bayan Gwamnatin Jihar Kogi ta rufe Masana’antar Simintin Dangote da ke Obajana a jihar.

Direbobin manyan motocin sun ce ba sa su janye ababen hawansu ba, har sai gwamnatin jihar ta bude masana’antar, wadda yanzu kwana uku ke nan da rufe ta.

Matakin da masu manyan motocin suka dauka ya tsayar da zirga-zirgar ababen hawa da sauran harkoki cik a hanyar da at sada yankin Kudanci da kuma Arewacin Najeriya.

Masu tirelolin sun tare hanyar a daidai lokacin da hanyar Koton-Karfe ke fama da matsalar ambaliya na kuasn mako guda, lamarin da ya kara jefa matafiya cikin tasku.

Wani mai abun hawa da lamarin ya kawo wa tafiyarsa cikas ya dawo Lakwaja a ranar Juma’a, Malam Usman Odaudu, ya ce abin ya wuce misali.

“Muna fama da mummunar ambaliya da ta mamaye Gadar Koton-Karfei end da ke kan hanyar na kusan mako guda, da wahalar da hakan ke haifarwa.

“Yau da rana kuma direbobi da ke ikirarin zanga-zanga saboda rufe Masana’antar Simintin Dangote suka kawo motocinsu suka tare hanyar gaba daya, babu yadda abin hawa zai iya wucewa,” in ji shi a fusace.


  • Ya ce direbobin manyan motocin sun ce ba sa su janye ababen hawansu ba, har sai gwamnatin jihar ta bude masana’antar, wanda yanzu kwana uku ke nan da rufe ta.
  • Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *