May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Akwai tabbacin Asuu zata janye yajin Aiki a tsakanin Alhamis da Juma’a

1 min read

Wasu rassan kungiyar malaman jami`o`i a Najeriya, sun fara duba yiwuwar janye yajin aikin da suke ko kuma ci gaba.

Tuni rassan kungiyar suka gudanar da taruka domin yanke shawara a kan daukar matakin da ya dace.

A ranar Alhamis 13 ga watan Oktoba ne ake sa ran shugabannin rassan kungiyar za su kai ra`ayoyin rassan wajen taron da shugabannin uwar kungiyar za ta yi don daukar mataki na gaba.

Rassan kungiyar malaman jami`o`in sun yanke shawarar gudanar da tarukansu ne bayan shiga tsakanin da kakakin majalisar wakilan Najeriyar ya yi, wanda bayan ya gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya shaida wa `yan kungiyar cewa akwai haske sosai.

Tuni dai wasu rassan kungiyar malaman jami`o`in suka fara tattaunawa a matakin rassa da kuma shiyyoyi alamar da ke nuna cewa akwai bayanin da suka samu, wanda kuma suke yanke shawara a kan sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *