May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ba za mu cefanar da kamfanin dillancin wuta na kasa ba – Gwamnatin Najeriya

1 min read

Ba za mu cefanar da kamfanin dillancin wuta na kasa ba – Gwamnatin Najeriya

Najeriya ta ambato wata sanarwa da hukumar ta fitar, in da bukaci jama’a da su yi watsi da rahotannin da ke cewa za ta yi hakan.

Wannan dai martani ne ga rahotannin kafafen yada labarai da ke bayyana cewa gwamnati na shirin cefanar da kamfanin, inda rahotannin suka ce za a yi hakan cikin watanni masu zuwa.

”Gwamnatin tarayya ba ta da shirin sayarwa ko kuma cefanar da kamfanin dillancin wuta na kasa, kuma babu wani daga gwamnatin da ya sanar da hakan,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin tarayya karkashin mulkin shugaba Buhari na mayar da hankali kan zamanantar da bagaren wutan lantarki na kasar ta hanyar bijiro da tsare-tsare wanda ya hada da hadin gwiwa da shirin inganta wuta na ofishin shugaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *