May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Zamfara ta bude makarantu 45 da ta rufe a baya saboda barazanar tsaro,

1 min read

Gwamnatin Zamfara ta bude makarantu 45 da ta rufe a baya saboda barazanar tsaro
An dade ana ta kiraye-kirayen bude makarantu a jihar

An dade ana ta kiraye-kirayen bude makarantu a jiharImage caption: An dade ana ta kiraye-kirayen bude makarantu a jihar
Gwamnatin Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta sake bude makaranatu 45 cikin 75 da ta rufe a fadin jihar saboda matsalar tsaro.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ambato Sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi a jihar, Kabiru Attahiru na ya bayyana matakin lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin gaggawa kan ilimi a jihar a ofishinsa.

Attahiru ya ce gwamnati da jami’an tsaro na aiki tukuru domin tabbatar da cewa tsaro ya inganta a jihar.

”Muna sa ran kyautatuwar yanayin tsaro a Zamfara domin ganin mun bude sauran makarantu 30 da suka rage a rufe”, in ji Attahiru.

Gwamnatin Jihar Zamfara dai ta rufe makarantu a watan Satumban 2021 bayan garkuwa da daliban makarantar sakandaren Kaya da ke karamar hukumar Maradun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *