May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kwalara ta kashe mutum 233 a Najeriya

1 min read

Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya(NCDC) ta ce cutar kwalara ta kashe mutum 233 a jihohi 31 na ƙasar.

Sannan hukumar ta ce an samu jimillar mutum 10,217 waɗanda suka kamu da cutar ta amai da gudawa.

Shugaban hukumar Dr Ifedayo Adetifa ne ya bayyana hakan sa’ilin da ya yi bayani kan halin da ake ciki a ɓangaren lafiya na ƙasar a ranar Talata.

Ya ce a watan Agusta an samu ƙaruwar kimanin kashi 47% na yawan masu kamuwa da cutar idan aka kwatanta da watan Yuli da ya gabata.

A cewarsa ya zuwa yanzu an tabbatar da cewa mutane 933 sun kamu da zazzaɓin Lassa, yayin da zazzaɓin ya yi sanadiyyar rayukan mutane 173.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *