May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

ASUU Ta Janye Yajin Aikin Wata takwas

1 min read

Kungiyar Malaman Jami’a ta ASUU ta janye yajin aikin da ta shafe wata takwas tana gudanarwa a Najeriya.

Kungiyar ta yanke yanke shawarar janye yajin aikin ne a babban taron Majalisar Zartarwarta da ya gudana a Abuja.

Wani babban jami’in ASUU da ya halarci taron na cewa, “Gaskiya ne, mun janye yajin aikin… Na gaba da safiyar nan Shugaban ASUU na Kasa zai fitar da sanarwar a hukumance.”

Wata takwas cif ke nan da malaman jami’o’in gwamnati suka yi suna yajin aikin da kungiyar ta kira tun ranar 14 ga ga watan Fabrairu, 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *