May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ƴan bindiga na zafafa hare-hare a wasu sassa na Zamfara

2 min read

Al’ummar Ƙaramar Hukumar Bukkuyum a Jihar Zamfarar Najeriya na ci gaba da kokawa game da hare-haren da ‘yan bindiga suke kai musu.

Mazauna yankin sun ce yan bindigar sun hana su sukuni sakamakon irin ɗauki ɗai-ɗai da suke musu da hare-haren ba zata da suke kai musu.

Wani mazaunin yankin na Bukuyyum ya shaida wa BBC cewa ko a ranar Juma’a sai da ƴan bindiga suka sace ƴan uwansa goma sha ɗaya a Nasarawa Burkullu da ker yankin na Bukkuyum.

Haka kuma ya bayyana cewa ko a kwanakin baya sai da ƴan bindigan suka harbe wani yaro a garin.

Ya bayyana cewa kusan duka jama’ar da ke wannan yankin sun yi gudun hijira saboda bala’in ƴan bindigan.

Ya kuma ce a cikin Karamar Hukumar Bukkuyum ɗin sun sace shanu sama da 300 a ranar Juma’a.

Gwamnatin Jihar ta Zamafara dai ta bayyana cewa tana sane da abubuwan da ke faruwa a wannan yanki da wasu wuraren ma da ke makwaftaka da Bukuyyum.

Ibrahim Dosara shi ne kwamishinan watsa labarai na Jihar ta Zamfara ya kuma shaida wa BBC cewa akwai matakan da gwamnati ke ɗauka domin magance wannan matsala.

Ya bayyana cewa sakamakon wannan matsala majalisar tsaro ta jihar ta yanke shawarar rufe wuraren da lamarin ya shafa domin gudanar da wasu ayyuka.

Jihar Zamfara dai na daga cikin arewa maso yammacin Najeriya da ƴan bindiga suka addaba.

Ko a kwanakin baya sai da ƴan bindigar suka kashe mutum tara a Ƙaramar Hukumar Maru ta jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *