May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ana fargabar mutuwar mutum 33 a kifewar kwale-kwale a jihar Naija

1 min read

Akalla mutum 33 wadanda suka hada da mata da kananan yara ne ake tunanin sun mutu sakamakon kifewar wani kwale-kwale da ke dauke da fasinjoji fiye da 50 a kogin Kaduna a jihar Naija da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa kwale-kwalen ya taso ne daga kauyen Danchitagi da ke karamar hukumar Lavun zuwa kauyen Gbara da ke karamar hukumar Mokwa a jihar ta Naija ranar Juma’a da daddare.

Rahotonni sun ruwaito cewa hatsarin ya faru ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya hade da iska mai karfin gaske.

Tuni dai aka dauki wadanda aka kubutar zuwa asibitin kauyen Gbara domin ba su kulawar gaggawa.

Hatsarin kwale-kwale dai na neman zama ruwan dare a Najeriya, ko a ranar Litinin din da ta gabata ma a ƙalla mutum 76 ne aka bayar da rahoton mutuwarsu bayan hatsarin kwale-kwale a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Kwale-kwalen, wanda ke ɗauke da mutum 80, ya kife a yankin Ogbaru da ke jihar Anambran.

Mafi yawan wadanda abin ya rutsa da su mata ne da yara, da ke ƙoƙarin tsere wa yankinsu da ambliyar ruwa ta mamaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *