May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rufe kafofin yaɗa labarai da gwamnatin Zamfara ta yi ya saɓa doka – NBC

2 min read

Hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta Najeriya ta ce matakin rufe wasu kafofin yaɗa labarai da gwamnatin Jihar Zamfara ta yi ranar Asabar “ya saɓa wa doka”.

Shugaban hukumar ta National Broadcasting Commision (NBC), Balarabe Shehu Ilelah, ya ce sun sanar da gwamnatin Zamfara da ke arewacin ƙasar ƙarara “irin saɓa wa dokar da aka yi”.

“Mun faɗa wa gwamnati ta bai wa al’ummar jihar haƙuri,” a cewarsa cikin wata sanarwa. “Sannan mun shawarci jami’an tsaro da su share umarnin da aka ba su na hana ma’aikatan kafofin da abin ya shafa yin aikinsu na halali.”

A ranar Lahadi Kwamashinan Yaɗa Labarai na Zamfara Ibrahim Dosara ya faɗa wa BBC Hausa cewa an rufe gidajen labaran ne saboda sun yaɗa taron jam’iyyar adawa ta PDP duk da cewa gwamnatin jihar ta hana tarukan siyasa saboda dalilai na tsaro.

Ya ce Majalisar Tsaro ta Zamfara ce ta amince tare da ba da umarnin rufe kafofin labaran da suka ƙunshi Rediyo Najeriya, da Pride FM Gusau, da NTA Gusau, da Gamji Talabijin, da Vision FM, da Al Umma TV.

NBC ta ƙara da cewa “muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su guji kawo cikas ga ci gaban da aka samu na dimokuraɗiyya a Najeriya”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *