May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wasu dalibai sun ce Yajin Aikin Asuu ya zamar musu masifa

2 min read

Wannan yajin aiki na malaman jami’o’i ya yi matuƙar taɓa mu ɗalibai, don ni har sai da ta kai wani abokina ƙiri-ƙiri ya fara shaye-shaye saboda tsabar shiga damuwa,” in ji Ibrahim Yunusa, ɗalibi a Jami’ar Umaru Musa Ƴar adua a jihar Katsina.

Ibrahim ya ce ya lura abokin nasa, wanda ba zai so bayyana sunansa ba, ya fara tu’ammali da miyagun ƙwayoyi tun wata uku da fara yajin aikin, “wanda a da ba halayyarsa ba ce sam-sam”.

Ɗalibin ya shaida wa BBC Hausa hakan ne a wani shiri da ta nemi jin ra’ayoyin mutane kan muhimman fannoni da suka fi shafar ƴan ƙasar, gabanin zaɓukan 2023.

Matashin mai shekara 25, ya ce a sanin da ya yi wa abokin nasa wanda suke ƙut da ƙut, ko sigari ba ya sha, amma a yanzu abin na neman zarce hankali.

“Da na tuntuɓe shi don yi masa faɗa kan sabon halin da ya fara din, sai ya ce wai na ƙyale shi damuwa ce ta yi masa yawa.

“Ga dukkan alamu wasu sabbin abokai da ya fara bi ne suka ɗora shi a kan wannan hanyar, kuma duk rashin abin yi ne ya jawo hakan” ya ce.

Yawanci matasa kan samu kansu a yanayi na shaye-shayen ƙwayoyi ne sakamakon damuwa da suke samun kansu a ciki, ko rashin abin yi, al’amarin da ya zama ruwan dare a Najeriya.

dalibai
ASALIN HOTON,GETTY IMAGES
Bayanan hoto,
Dalibai sun ce yawan yajin aiki na jawo musu koma baya wajen kasa kammala karatu a kan lokaci

Tun watan Fabrairun shekarar 2022 ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya ta shiga yajin aiki, kuma an shafe watanni ana cikinsa.

Ba Ibrahim da abokinsa kawai yajin aikin ya yi wa mummunan tasiri ba, gomman ɗalibai ne suka rubuto wa BBC Hausa yanayin da yajin aikin ya jefa su a ciki.

Kuma duk da cewa akwai ɗumbin jami’o’in kudi masu zaman kansu a ƙasar, ba kowane zai iya biya ba.

Ibrahim wanda a yanzu ya kama kasuwanci ka’in da na’in don rufa wa kansa asiri kafin a janye yajin aikin, ya ce yana iya bakin ƙoƙarinsa don fitar da abokin nasa daga halin da ya shiga ta hanyar yi masa nasiha.

“Aji uku muke a jami’a, ai ba zai yiwu na sa ido damuwa ta hana mu ƙarashe wahalar da muka fara ba wacce muke sa ran za mu ci ribarta a gaba,” ya ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *