July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Akwai fargabar aikata kisan kiyashi a yankin Tigray – Shugaban WHO

1 min read

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce akwai fargabar za a aikata kisan kiyashi a yankin Tirgay na Habasha.

Dakta Tedros wanda shi ma dan asalin yankin na Tigray ne ya ce mutum miliyan shida ne ke fuskantar hare-hare ba tare da sun iya fita ba tsawon kusan shekara biyu.

Ya fada wa manema labarai a Geneva cewa Duniya ba ta mayar da hankali kan yankin Tigray kamar yadda ya kamata ba.

Sai dai gwamnatin Habasha ta soki Dakta Tedros, inda ta ce shi kansa ya gaza tabuka komai kan lamarin.

A farkon makon nan ne dakarun Habasha da na Eritrea da ke mara musu baya suka kwace iko da birnin Shire.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *